Friday, November 11, 2016

Anyi ma magidanci tonan silili kan satar tukunyar miya

Wani magidanci uban yaya biyu ya shiga tasko yayin da yan banga suka kama shi a karamar hukumar Yenagoa na jihar Bayelsa kan laifin satar wata tukunya cike da miya, malmalan tuwo 12 da rabin bahon garri.

Barawon

Yan banga ne suka kama Magidancin mai shekaru 35 mai suna Kaduna Enatimi da misalin karfe 2 na daren ranar Alhamis 10 ga watan Nuwamba yayin da yake tsakiyar more abincin daya sata tare da sharbar miyar, a cewar rahoton jaridar Punch.

Barawon yayi ta yi ma yan bangan magiya yana basu hakuri, kuma ya danganta laifinsa da yunwa data yawaita a kasar nan hadi da lalacewar tattalin arziki.

Shugaban kwamitin ya bangan Cif Moneysweet Asomo yace sun kama barawon ne yayin dayake tsakar more kayan daya sata daga wani shagon siyar da abinci mallakan wata mata yar kasuwa yar asalin jihar Akwa Ibom.

MoneySweet ya cigaba da cewa “muna cikin sintiri da misalin karfe 2 na daren alhamis, a lokacin da muka isa kusa da makarantar Timida, sai muka ci karo da wannan mutumim a shagon siyar da abinci. Shagon mallakan wata mata ce yar asalin jihar Akwa Ibom wadda aka fi sani da suna Uwargida Blessing, daga nan sai muka fara yi masa tambayoyi, inda ya amsa cewar sato tukunyar miyan yayi, tare da wasu malmalan tuwo da rabin bahon garri”

Asomo yaci gaba da bayyana yadda suka kwashe da barawon, inda yace “barawon yayi ikirarin halin matsin rayuwa ne ya sanya shi aikata laifin”

Sai dai rahotananni sun bayyana cewar shugaban majalisar sarakunan gargajiyan masarautar Epie yankin Obenibe XI Epie Sarki Hope Adike ya sanya baki cikin lamarin, inda ya umarce yan bangan dasu fito da barawon fili kowa ya ganshi, tare da ababen daya sata, don hakan ya zamto izina ga sauran mutane.

Bayan an bayyana shi ga jama’a ne sai aka sake shi ya kama hanyarsa ya tafi. A wani labarin kuma, wani tsohon banza mai shekaru 75 ya bayyana yadda ya mayar da yayansa su 14 yan fashi da makami. Rahotanni sun bayyana cewar tsohon mai suna Malam Yahaya Shanjiri ya amsa laifinsa da kansa.

Shanjiri ya bayyana haka ne a lokacin da wasu miyagun mutane da suka tasan ma 5000 suka nemi gafarar jama’ar jihar Neja, yace ya dade yana aikata muyagun ayyuka daban daban sama da shekaru 30. Sai dai acewarsa bayan yayi murabus ne ya fara horar da yayansa don su gaje shi.

Source: Naij Hausa

Labels: ,

0 Comments:

Post a Comment

Subscribe to Post Comments [Atom]

<< Home