Dalilin da zai sa yara 70,000 su mutu a Najeriya cikin 2017 da kuma abunda ya zama dole ayi- Watkins
– Talauci zai kasance babban kalubale a sansanin yan gudun hijira daban-daban a arewa maso gabas nan bada jimawa ba
– Wani kungiyar taimako, na ceton yara, na rokon kasashen waje da su zo su taimaki yara a sansanin
Yara na cikin hatsari a sansanin yan gudun hijira har sai kasashen waje sun taimaka
Kasar Najeriya na cikin hatsarin rasa kimanin yara 70,000 a shekara ta 2017, kungiyar agaji, na ceton yara, ta bayyana a yayinda take rokon kasashen waje da suyi gaggawan taimako gurin yaki da yunwa, tamowa da cututtuka a kasar.
Aikin ta’addanci yafi illata yara da kuma wadanda ke sansanin yan gudun hijira a fadin arewa maso gabashin Najeriya, a cewar wata rahoto daga jaridar Daily Trust.
Rahoton ya nuna kalamin shugaban kungiyar na taimakon yara a Amurka, Kevin Watkins, cewa yayi roko na musamman kan cewa kasashen waje su shigo lamarin don su tallafi gwamnatin Najeriya da kayayyaki domin ceto rayukan jama’a da yawa.
Source Naij Hausa
0 Comments:
Post a Comment
Subscribe to Post Comments [Atom]
<< Home