Tuesday, November 15, 2016

Ghana: An bude katafariyar gadar sama a Accra

An bude sabuwar katafariyar gadar sama mai rassan titina, a Accra, wadda ake sa ran za ta kawo karshen wahalar da ake sha kullum ta cunkoson ababan hawa a babban birnin na Ghana.


Shugaba John Mahama, wanda ya bude gadar, wadda aka sanya wa sunan Kwame Nkrumah (Kwame Nkrumah Interchange), ya ce, ita ce gadar sama mafi tsawo da nisa a duk yammacin Afirka.

A tsakiyar katafariyar gadar wadda kafar labaran Joy News ta ce an kwaikwayo ta ne daga Dubai, an gina wani wurin shakatawa da ruwa ke tsiri yana sauka, mai kayatarwa da ban sha'awa.

A yayin bude gadar Shugaba Mahama ya ce, ''ba wai hanya ce kawai ta zamani ba, wuri ne mai kyau ga 'yan yawon bude idanu.''

Ya kara da cewa, ''lafiya da kuma farin cikin 'yan kasar abubuwa ne da su ma su ke da muhimmanci.''

Shugaban ya bukaci jama'a da su rika zuwa wannan wurin shakatawa da ke tsakiyar gadar domin hutawa da nishadi.

Aikin wanda ya dauki shekara uku kafin a kammala shi, ya kunshi titunan sama da dama da suka hada yankin tsakiyar babban birnin, mai fama da cunkoson ababan hawa da jama'a, da sauran sassan birnin.

Tsawon shekaru jama'a ke fama da matsalar cunkoson ababan hawa, lamarin da ke bata musu lokaci a kullum.

Source: BBC Hausa

Labels:

0 Comments:

Post a Comment

Subscribe to Post Comments [Atom]

<< Home