Saturday, November 26, 2016

[Kali] Yadda Zakayi Install Kali Linux A Kowacce Irin Wayar Android Kashi Na Daya

Assalamu Alaikum Jama'a Barkanmu Da Sake Saduwa Daku A Wannan Sabon Darasin Mai Bayani Akan Yadda Zakayi Installing Kali Linux Akowacce Irin Android Phone.

Duba Gabatarwa Gameda kali Linux Anan...

Batare Dana Cikaku Da Wani Dogon Bayaniba Bari Muyi Abunda Yakawomu.

Kali Linux Software Ce Tayin Hacking Na Abubuwa Dadama, Wanda Aka Sanya Mata Ka-Yayyakin Hacking Har Guda Dari Uku Da Talatin [330 Hacking Tools] A Turance Kenan.

Daga Cikin Irin Hacking Tools Din Sune Kamar Haka:

  • Metasploit
  • Sqlmap
  • Sqlninja
  • Darkmysqli
  • Sqlbrute
  • WPscan
  • OWASP
  • Uniscan
  • Nikto
  • Wireshark
  • Aircrack-ng
  • Burpsuite
  • TheHavester
  • Xsser
  • John The Ripper
  • Cupp.
Dadai Sauransu....

Abubuwanda Ake Bukata Wajan Sanya Kali Linux A Wayarka Sune:

1. Kayi Rooting Na Wayarka
2. Kasamu Memory 8GB.
3. Dauko Complete Linux Installer
4. Dauko Busy Box Pro
5. Dauko Vnc Viewer
6. Dauko Terminal Emulator

Katabbatar Kayi Rooting Na Wayar Taka Kafin Kafara Kokarin Sanya Kali Linux A Wayarka, Idan Kuma Bakayiba To Zaka Iya Shiga Nan Kayi Domin Sanin Yadda Zakayi Rooting Na Wayar Taka.

Bayan Nan Saika Dauko Duk Wadannan App Din Dake Sama Kayi Installing Nasu Daya Bayan Daya Bayan Kagama Installing Din, Saika Bude Busy Box Zakaga Install Da Uninstall Saika Dannan Akan Install Kamar Wannan Hoton Dake Kasa:


Bayan Yagama Installing Saika Kulleshi, Kabude Complete Linux Install Kashiga Install Linux Manually Kamar Haka:


Saika Zabi Kali Linux Kamar Haka.


Saika Shiga Download Image Kamar Haka:


Bayan Kagama Download, To Saikayi Unziping Nashi Zakagansu Kwara Biyune Da kalilinux.ext2.img Dakuma kalilinux.ext2.img.md5 Nauyinsu Zaikoma 3.26GB To Saika Hada Sabuwar Folder A Memory Dinka Saika Sanyasu Acikin Folder Din.

Saika Bude Complete Linux Installer Dinka, Zakaga Launch Linux Kamar Wannan Hoton Dake Kasa Saika Shiga.


Saika Zabi Kali Zakaga Sufana Daga Sama Saika Shiga Kamar Wannan Hoton Dake Kasa:


Zakaga Edit Saika Shiga Bayan Kadannan Yabude Zakaga Wani Wuri Da Alamar Kamar Wannan Hoton:


Saika Shiga, Bayan Yabude Zakaga Sunan Folders Din Wayarka To Saika Dubo Wannan Folder Din Daka Hada Mai Suna Kali Saika Shiga, Bayan Tabude Zakaga Wannan Files Din Daka Sanya Aciki Sai Kaza6i Kalilinux.img Saika Danna Ok Kamardai Yadda Kukaga Wannan Hoton Dake Kasa.


Zakaga Yabude Maka Wani Page Saika Shiga SAVE CHANGES Kamar Yanda Kuka Gani A Wannan Hoton Dake Kasa.


Zakaga Yasake Bude Maka Wani Page Wanda Zakaga Start Linux Saika Danna Kawai Akansa Kamar Wannan Hoton Nakasa.


Kana Dannawa Akai Zakaga Yawuce Dakai Zuwa Terminala Emulator Kamar Wannan Hoton Dake Kasa.


Saika Rubuta vncserver Saika Dannan Enter, Zakaga Yadanyi Wasu Rubututtuka Dakansa Bayan Yagama Saikayi Minimize, Kabude VNC Viewer Zakaga Wani Alamar + Saika Danna Akai.

Zakaga Yabude Maka Wani Page Saika Sanya Address Dakuma Name Saika Dannan Akan Create Kamar Wannan Hoton Dake Kasa.


Bayan Yabude Zaka Zaka Inda Akasa Connect Daga Kasa Saika Shiga Kamar Wannan Hoton Nakasa.


Bayan Yabude Zakaga OK Daga Sama Saika Dannan Akai Kamar Wannan Hoton Nakasa.


Bayan Yabude Zakaga Inda Zaka Rubuta Password Saika Rubuta kalilinux Saika Shiga Continue Kamar Wannan Hoton Dake Kasa.


Yana Budewa Zakaga Kali Linux Yabude Lafiya Lau Awayarka....

Kamar Yadda Kukaga Wannan Hoton Nakasa.


Shikenan Kayi Installing Kali Linux A Wayarka Sauran Aiki Dashi Kawai Yarage Maka. Saikuma Mun Hadu Adarasi Nagaba Akan Yadda Zaka Fara Aiki Da Kali Linux Bayan Kayi Installing Dinsa.....

Idan Kuma Akwai Mai Wata Tambaya To Zaka Iyayi Insha ALLAHU Za'a Baka Amsa Bada Jumawaba....

SHARADI!!! Banyi Wannan Bayani Dan Kakoya Kaje Kacutarda Waniba Ko Wata Nayisane Dan Ilmantarwa Kadai, Idan Kayi Amfani Dashi Ta Wata Hanya Wadda Bata Daceba, Wani Abu Yafaru Dakai Babu Ruwana Karma Kace Kasanni....

[!] =======================
[!] Rubutawa Da Hada Hotuna.
[!] Sunusibrowser Strygwyr
[!] Daukar Nauyi 24wikis.com
[!] =======================

Labels: ,

0 Comments:

Post a Comment

Subscribe to Post Comments [Atom]

<< Home