Thursday, November 10, 2016

Labarai: Goodluck Jonathan ya yabawa Hillary Clinton akan amincewa da zabe

– Tsohon shugaban kasar Najeriya Dakta Goodluck Jonathan ya sara wa Hillary Clinton da amincewa da sakamakon zaben Amurka

– Jonathan yace Amurka ta hada kanta kuma a cigaba


Tsohon shugaban kasan Najeriya, Goodluck Jonathan, ya tofa albarkacin bakinsa akan zaben kasar Amurka inda ya yabawa Hillary Clinton da amincewa da sakamakon zaben.

A wata zaben da aka siffanta da abun haushi, Trump ya lallasa Clinton a zaben da ya gudana a ranan 8 ga watan Nuwamba.

A wata saka da ya daura a shafin sada ra’ayi da zumuntarsa, Goodluck Jonathan ya taya Trump murna kuma ya yabi Clinton.

Yace: “Ina taya yan America murna da zaban Donald J. Trump ,kuma in ayabawa Hillary Clinton da amincewa da sakamakon zaben. Bayan nayi irin wannan nima, na san irin karfin halin da mutum ke bukata wajen yin hakan. Nayi farin cikin game da maganan da Trump yayi na cewa Lokaci yayi mu hadu tare.

A karshe, wajibi ne in yaba wa yadda aka gudanar da zaben Amurka, sun raba kan su kuma yanzu suna hada kansu. Ina musu fatan Alheri kuma Ubangiji ya taimaka.”

Hakazalika shugaba Muhammadu Buhari ya taya Donald Trump murna akan nasararsa a zaben Amurka.

Yace: “Ina sa ran aiki tare da sabon shugaban kasa Trump domin karfafa alakar abotan da muka fara, irinsu hadin kan kasa-kasa kamar yaki da ta’addanci, zaman lafiya, tsaro,tattalin arziki,demokradiyya da shugabanci mai kyau.”

Source: Naij Hausa

Labels: ,

0 Comments:

Post a Comment

Subscribe to Post Comments [Atom]

<< Home