Matar Wani Daya Gama Karatu Bai Samu Aikin Yiba Ta Haifa Masa Yara Uku
Yara dai kyautane daga ALLAH, a inda wasu suke rokon ALLAH ya basu haihuwa, wasu kuma haihuwar tana zuwa musu ne ba zato babu tsammani.
ma’auratan da Allah bai basu haihuwa ba, suga wasu iyayen suna wulakanta yaransu ko kuma su dunga wurgar da yaran da suka haifa da kansu. Wasu matan akullun addu’ar su itace su zama iyayen wasu, musamman idan suka ga irin wa’ancan iyayen wa’anda basu kulawa da yaran su.
Haka kuma, abin tausayine kwarai, domin
kuwa haka rayuwa take saboda rayuwa bata samun abinda takeso ko yaushe. Wani kuma Allah yakan bashi haihuwan saidai kuma baida abinda zai tarbiyartan da yaran nasa.
Kuma akan dalilin hakan, bai kyautuwa
kacema mutanen da basu da kudi dasu daina haihuwa harsai sun sami kudin da zasu tarbiyartar da yaran nasu.
Haka anan, wani daya gama karatunsa a
Najeriya bai samu aikin yiba, Matar sa ta haifa masa yara uku, duk da bai samu aikin da zaiyi ba. Saboda da haka rashin aikin yi, bashi ke nufin cewar Allah bazai iya yi maka wata kyauta ba a rayuwar ka.
Haka kuma, haihuwar yan ukun da akayima Mr Kunle, ya sanya wasu mutane yin kira da a taimaka ma ire-iren su da basu da aikin yi, domin kuwa sun gama karatun su. Matar Mr kunlen dai ta haifa masa yara uku ne duk da cewar baida aikin dazai kula da tarbiyar yaran nasa.
Dalibin dai wanda ya gama jami’ar Ibadan yana neman aikin yi yanzu sosai saboda ya kara samun nauyin mutanen da suke a karkashin sa domin daukan nauyin su.
Haka kuma, mutanen Najeriyan nan masu
tausayi sun tausayama wannan bawan Allah inda suka fara taimaka masa. Babu mamaki haihuwar yaran nan ya sanya mutumin ya fita daga cikin matsalar dayake ciki na rashin aikinyi, ya sanya masa farin ciki a rayuwar sa.
0 Comments:
Post a Comment
Subscribe to Post Comments [Atom]
<< Home