"Al- Mustapha ya bada gudummuwa wajen kisan Kudirat Abiola"
β Har yanzu kuruwar Kudirat, matar marigayi Moshood Abiola wadda ake zargin sojoji suka kashe ta bata huta ba yayin da sabbin bayanai ke fitowa
β Manjo Hamza Al- Mustapha da iyalan Abiola na ci gaba da cece-kuce yayin da iyalan Abiola kema Al-Mustapha tuni game da ikrarin saje Rogers
β 24wikis.com ta sake duba faifan bidiyo na ikrarin saje Rogers wanda yayi ma hukumar Oputa koko Oputa Panel wanda tsohon shugaba Olusegun Obasanjo ya kafa
Iyalan marigayi Moshood Abiola wanda ake zaton shi ya lashe zaben shugaban kasa na 12 ga Yuni 1995 a Najeriya na maida martani kan zancen manjo Hamza Al-Mustapha mai murabus game da kisan Kudirat Abiola.
Ana zargin gwamnatin mulkin soja ta Sani Abacha da kisan yayin da take yima mijinta wanda ke tsare yaki.
Al-Mustapha wanda tsohon dogari ne na Abacha ya nisanta kai nai da kisan matar da βyan rajin kishin dan adam ke ma biki a kowace shekara.
A wata wasika zuwa ga Al-Mustapha, iyalan Abiola na yi masa tuni game da ikrarin saje Rogers, sojan da aka sa ya kashe matar. A wajen hukumar bincike ta Oputa koko Oputa panel, Rogers yayi ikrarin cewa Al-Mustapha ya bashi bindigar daya kashe Kudirat da ita.
Source: Naij Hausa
0 Comments:
Post a Comment
Subscribe to Post Comments [Atom]
<< Home