Monday, November 14, 2016

Shi'a: An kashe mutum goma a Katsina


Rahotanni daga jihar Katsina da ke arewacin Najeriya sun ce an kashe akalla mutum goma lokacin da 'yan kungiyar 'yan uwa Musulmi wadda aka fi sani da Shi'a suke juyayin ranar Ashura.

Bayanan da manema labarai suka samu sun ce lamarin ya faru ne a garin Funtua, lokacin da 'yan sanda da sojoji suka yi yunkurin hana 'yan Shi'ar yin tattaki da suka saba yi duk shekara domin tunawa da ranar ta Ashura.

Wani ganau ya shaida wa manema labarai cewa ya kirga gawarwakin mutum takwas.

Sai dai babu wata majiya mai zaman kanta da ta tabbatar da wannan ikirari.

Ya kara da cewa an jibge jami'an tsaro a kusa da wurin da suke yin tattakin domin hana su, yana mai cewa jami'an tsaron sun rika harba bindiga sama domin tsorata jama'a.

Da ma dai jihohin Kaduna da Kano da kuma Katsina sun hana 'yan Shi'a yin tattaki a wannan shekarar.

Hasali ma, jihar Kaduna ta haramta kungiyar saboda zarginta da keta dokoki da kuma tayar da zaune tsaye, zargin da suka musanta.

Ashura a Kaduna:
An tsaurara matakan tsaro a Kaduna a lokacin da ake kyautata zaton yan kungiyar Islamic movement mabiya mazhabar shia za su yi muzaharar ranar Ashura.

Wakilinmu da ke Kaduna, Nura Muhammad Ringim ya ce 'yan sanda da sojojin jihar, har ma da tankokin yaki sun ta yin sintiri a garuruwan da ke Kaduna da Zaria, inda nan ne hedikwatar kungiyar.

Duk dai yan kungiyar ba su sami damar gudanar da muzahara kamar yadda suka saba ba,rahotanni na cewa an kona gidan shugaban kungiyar, Malam Mutari Sahabi da ke Unguwar Tudunwada da ke jihar Kaduna.

Bayanai na nuna cewa matasa yan unguwa ne suka kona gidan shugaban kungiyar ta yan Shia da ke jihar.

Bayan nan ne kuma aka ce matasa sun ci gaba da wawashe kayan gidan da ba su kone ba.

An tabbatar cewa mutane biyu sun rasa rayukansu..

Ashura a Kano:

Wakilinmu na Kano, Mukhtar Adamu Bawa ya ce an samu dan hargitsi bayan mabiya mazhabar Shi'a a Kano sun kammala tattakin da suka shirya.

daga nan kuma sai wasu mutane da ba a iya tantance ko su wane ne ba suka rinka bin mutane suna kai mu su hari.
Sai dai kuma ba a samu rahotannin da ke nuna an rasa rai ba a Kano.

Mene ne Ashura?
Mabiya mazhabar Shi'a a duk fadin duniya suna amfani da ranar goma ga watan Maharram domin nuna bakin cikinsu ga rasuwar jikan manzon Allah, Imam Hussain.

'Yan Shi'ar dai sun yi amannar cewa a wannan rana ce Yazid wanda da ne ga Mu'awiyya, shi ya kashe Imam Hussain a shekarar 680AD.

Mabiya akidar Sunna dai sun yi imanin cewa Mu'awiyya ne sahabin annabi Muhammad SAW na biyar, bayan wafatin sayyid Ali.

Kuma mabiya sunnar suna musanta ikrarin na 'yan Shi'a da cewa Yazid ne ya kashe Imam Hussain.

Labels: ,

0 Comments:

Post a Comment

Subscribe to Post Comments [Atom]

<< Home