Nigeria: Kotu ta umarci gwamnati ta saki El-zakzaky
Wata kotun tarayya da ke birnin Abuja ta umarci hukumomin tsaron Nigeria da su saki shugaban kungiyar Islamic Movement of Nigeria ta 'yan Shi'a Sheikh Ibrahim El-zakzaky.
Kotun ta bukaci a saki El-zakzaky nan da kwanaki 45 ba tare da wani sharadi ba.
Alkalin kotun Kolawale Gabriel ya ce tsarewar da hukumomi ke cigaba da yi wa El-zakzaky tun watan Disamban bara haramtacciya ce kuma ba ta da hujja a karkashin dokokin kasar.
Haka ma ya umarci hukumomin da su biya shi da matarsa kudi Naira miliyan 50 a matsayin kudin fansa na tsare sun da aka yi a haramce.
A shekarar da ta gabata ne dai sojojin Najeriya suka kama shugaban 'yan Shi'ar bayan wata arangama da magoya bayansa a Zaria da ke arewacin kasar.
Akalla magoya bayansa 349 jami'an tsaro suka kashe a lokacin tarzomar.
Kungiyoyin kare hakkin bil'adama na gida da waje sun yi Allah-wadai da lamarin, sai dai sojojin sun kare matakin da suka dauka.
Source: BBC Hausa
0 Comments:
Post a Comment
Subscribe to Post Comments [Atom]
<< Home