Monday, November 14, 2016

Da Trump da Hillary duk daya ne inji Shekau

– Shugaban daya daga cikin bangarorin kungiyar Boko Haram biyu da ake da su a Najeriya ya ce ko da Hillary Clinton Amurkawa suka zaba a zaben shugaban kasa na makon jiya sun yi hasara.

– A cikin wani sakon murya da wani makusancinsa ya aiko wa majiyar mu, Abubakar Shekau ya ce a shirye suke su kalubalanci manufofin zababben shugaban na Amurka.


The fear of reprisal attacks

Ya kuma yi Allah-wadai da matakin da ya ce sarkin kasar Saudiyya mai bin tsarin shari’ar musulunci ya dauka na yin maraba da zaben Mr. Trump.

Ya yi amfani da wannan damar wajen daukar alhakin kai munanan hare-hare kan dakarun Najeriya a wasu sassan jihar ta Borno a kwanannan wanda ya hallaka da dama daga cikinsu.

A wani labarin kuma, Rahotanni na nuna cewa Mayakan Boko Haram sun mika kawunan su da iyalan su, sun kuma ajiye makaman Yaki. ‘Yan Boko Haram din sun mika kan su ne a Kasar Chad cikin wata daya zuwa biyu da suka wuce.

Majiya daga Gidajen Tsaro da ma Majalisar Dinkin duniya-UN suka tabbatar bayyana haka. An bayanna cewa daruruwan Mayakan na Boko Haram sun ajiye kayan yaki, sun ce ba su yi a Kasar Chad. A baya dai Boko Haram ta kashe mutane kimanin fadin Kasar Belgium ta Turai. Boko Haram din ta dade tana barna a Yankin na su Chad da kewaye.

Majiyar ta nuna cewa da alamu ana samun nasara a Yakin da ake yi da Boko Haram. Bincike ya nuna cewa wadanda aka dauka cikin Kungiyar ne kwanan nan suka ajiye makaman. Yanzu Boko Haram ta rasa mafi yawan iyakan iko a Kasar Najeriya. Ba a taba samun mayakan na Boko Haram sun mika kan su da yawa kamar wannan karo ba.

Kanal Mohammed Dole, wanda ke magana da Bakin Rundunar Hadin Gwiwa na MNJTF yayi wannan bayani a Babban Birnin Ndjamena. Yace mayakan Boko Haram 240 sun ajiye Makaman su.

Labels:

0 Comments:

Post a Comment

Subscribe to Post Comments [Atom]

<< Home