Labarai: Kungiyoyin sa kai sun sami horon dabarun tattara asiri game da boko haram
– Masu sa kai wadanda ke jihohin Adamawa da Taraba zasu sami horo kan yadda ake tattara bayanan asiri
– Hukumar ‘yan sandan Najeriya ta bada horon kwanaki biyar ga ‘yan kungiya 251 kan tattara bayanan asiri
– Horon zai karfafa guyoyin ‘yan kungiyar sa kan game da wasu dabaru
A kokarinta na dakile ayyukan Boko Haram, hukumar ‘yan sandan Najeriya ta bayar da horo na kwanaki biyar ga mambobi 251 na kungiyoyin sa kai a Jihohin Adamawa da Taraba kan tattara bayanan sirri. Kungiyoyin sa kan sun hada da mafarauta wadanda ke da muhimmanci ga sojojin Najeriya cikin yakin da ake yi da Boko Haram.
Horon na kwanaki biyar zai taimaki mafarauta su kware kan dabarun tattara asiri. Ranar Laraba 9 ga Nuwamba, Murtala Aliyu wanda shine kwamanda na ‘yan sa kai na jihar Adamawa ya fada a wani sansani na 14 na ‘yan sandan ko ta kwana dake Yola cewa horon nada muhimmanci.
Aliyu yace horon zai karfafa guyawun mambobin na ‘yan sa kai wajen aiki ingantacce domin taimakama ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro wajen yakin da ake yi.
Source: Naij Hausa
0 Comments:
Post a Comment
Subscribe to Post Comments [Atom]
<< Home