Zubar hawaye: An binne yara 6 bayan kishiyar uwarsu ta basu guba a Anambra (hotuna)
Al’amarin bakin ciki ya tsinkayi al’umman Ekwulumili a karamar hukumar Nnewi South dake jihar Anambra, yayinda yan uwan juna guda shidda suka mutu bayan sun ci guba
A cewar Ewenike Ogechukwu wanda ya yada hotunan jana’izar a shafinsa na Facebook, har yanzu ba’a san wanda ya aikata mugun aikin ba.
Ya kuma rubuta cewa yan sanda sun rigada sun ziyarci inda al’amarin ya faru sun kuma fara gudanar da bincike.
Ga abunda ya rubuta kamar haka: “Wani da ba’a san ko wanene ba ya sanya wa yaran guba a cikin abinci da suka ajiye a gida a Ekwulumili, jihar Anambra.
Amma a yanzu ana gudanar da bincike mai tsanani, dole ne a fito da wanda ya aikata wannan mugun ta’addancin don a hukunta shi daidai da laifinsa.”
Wani dan garin kuma mai suna Chidozie Venantiu ya kai kafofin zumunta don nuna tausayawarsa kan al’amarin ya kuma bukaci a taimakawa iyayen yaran.
Ya rubuta: “Garin na cikin tafasa tun jiya. Wani ahli sun rasa yara shidda bisaga abunda aka bayyana a matsayin gubar abinci.
Iyayen yaran na so su kashe kansu. Dan Allah ku taimaka ku tura wannan bayanin ga hukumar da ta dace.”
Wadanda suka mutu sun hada da Chukwuebuka, mai shekaru 17, Chinemere, 15, Afomachukwu, 13, Chekwubeckwu, 11, Onyekachukwu, 13 da kuma Chukwuziterem, 7.
A halin yanzu ba kowa bane ya yarda da cewan wani ne daban ya kashe yaran. Ana rade-radin cewa kishiyar uwar yaran c eke da alhakin kashesu ko kuma mahaifinsu yayi tsafi dasu.
Daga Naij Hausa
0 Comments:
Post a Comment
Subscribe to Post Comments [Atom]
<< Home