Monday, November 14, 2016

Kasar Mexico ta doke Amurka da ci 2-1 a wasan neman cancantar shiga gasar cin kofin duniya

-Kasar Mexico ta doke Amurka da ci 2-1 a wasan neman cancantar shiga gasar cin kofin duniya.

-Kyaftin din Mexico Rafael Marquez ne ya zuwa kwallon da ta ba su nasara a minti na 89.


Wasan wanda aka yi a Columbus, jihar Ohio ya zo da wani batu domin kuwa an yi shi ne bayan Donald Trump, mutumin da ya sha alwashin gina katanga tsakanin Amurka da Mexico, ya lashe zabe.

Mexico ta ci kwallonta ta farko ne ta Miguel Layun, kodayake dan wasan Bobby Wood ya farke bayan an dawo daga hutun rabin lokaci.

Nasarar da Mexico ta yi ta kawo karshen kashin da suka sha sau hudu a Ohio – jihar da take da muhimmanci, kuma wacce Trump ya ci zaben ta – domin kuwa tun shekarar 2001 suke kokarin cin wasa a jihar.

A wani labarin makamancin wannan ma, Tawagar kwallon kafa ta Nigeria ta doke ta Aljeria da ci 3-1 a wasan shiga gasar cin kofin duniya da suka fafata a filin wasa na Uyo da ke Akwa Ibom a ranar Asabar.

Nigeria ta fara cin kwallo ta hannun Victor Moses a minti na 26 da fara tamaula, sannan kyaftin din Super Eagles, John Mikel Obi, ya ci ta biyu daf da za a je hutu.

Bayan da aka dawo ne Algeria ta farke kwallo daya ta hannun Nabil Bentaleb, sai dai daf da za a tashi Victor Moses ya ci wa Nigeria kwallo na uku kuma na biyu da ya ci a fafatawar.

Daya wasan na rukuni na biyu tsakanin Kamaru da Zambiya tashi suka yi kunnen doki 1-1.

Da wannan sakamakon Nigeria ce ta daya a kan teburi da maki shida, sai Kamaru ta biyu da maki biyu, yayin da Zambia da Algeria ke da maki daya-daya.

Nigeria za ta karbi bakuncin Kamaru a ranar 27 ga watan Agustan 2017, inda a ranar ne Algeria za ta ziyarci Zambia.

Source: Naij Hausa

Labels:

0 Comments:

Post a Comment

Subscribe to Post Comments [Atom]

<< Home