Nigeria: 'Mun shafe kwana 10 muna kirga kudin sata'
Wani manajan banki a Nigeria ya bayyana yadda aka yi amfani da wasu jirage biyu makare da kudade wurin safarar kudaden da ake zargin na sata ne da ake shari'a a kansu.
Sunday Oluseye ya shaida wa wata kotu a Abuja cewa, yawan kudin -wadanda suka haura naira biliyan biyu- sun yi yawan da sai da aka shafe kwana 10 ana kirga su.
Yana bayar da shaida ne a wurin wata shari'a da ta shafi yadda wasu tsaffin jami'an gwamnati, suka wawure miliyoyin kudade.
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC, ta rawaito Manajan yana baar da shaida a kotu, cewa;
"Na tsorata lokacin da na ga yawan kudaden da jiragen suka kawo"
Ya kuma kara da cewa, yawancin takardun kudin 'yan naira 500 ne da 1,000.
Najeriya ta yi kaurin suna wajen cin hanci da rashawa, kuma kawo yanzu mutane kalilan ne Hukumar ta EFCC ta iya samu da laifi a gaban kuliya.
Source: BBC Hausa
0 Comments:
Post a Comment
Subscribe to Post Comments [Atom]
<< Home