Za’a kammala aikin hanyar Legas-Ibadan, inji Fashola
Ministan aiki da, lantar da gidaje Babatunde Raji Fashola yace nan bada dadewa ba za’a kammala aikin fadada babban titin Legas zuwa Ibadan.
Jaridar The Nation ta ruwaito Fashola yana bayyana haka a lokacin dayake bada bahasin yadda ya tafiyar da akalar ma’aikatarsa cikin shekara guda daya kwashe a matsayin minista.
Ministan yace za’a rufe katafaren gadar dake kan iyakar jihohin Legas da Ogun saboda aikin da ake gudanarwa a yankin.
Idan aka kyale hanyoyi haka, zasu dinga lalacewa ne, don haka akwai bukatar gyaransu da yi musu kwaskwarima akai akai, nji Fashola.
Fashola ya kara dacewa gwamnati na duba yiwuwar dakatar da manyan ababen hawa daga bin titunan, sakamakon nauyinsu yayi ma titin yawa. Sa’annan yace kamata yayi a gina sabbin gidan ajiye manyan ababen hawa don rage nauyin da manyan motoci ke dauka.
A wani labarin kuma hukumar kare haddura a kasa (FRSC) ta bayyana cewar zata karkatar da matafiya masu fitowa daga Legas zuwa Ibadan zuwa hanyar Ibadan zuwa Legas sakamakon aikin hanyar.
Hakan zai sanya rufe hanyar Legas zuwa Ibadan, zuwa Sagamu. Hanyar zai kwashe kwanaki bakwai a rufe, daga 16 ga watan Nuwamba zuwa 23. Sa’annan hukumar tace kamfanin Julius Berger zata rufe wani bangare na babban titin Ibadan-Legas.
Matafiya da dama sun nuna damuwarsu dangane da rufe hanyar, amma hukumar FRSC ta sake fitar da wata sanarwa inda take baiwa jama’a tabbacin hana cunkoso a kan hanyar duk da aikin dake gudana.
Source: Naij Hausa
0 Comments:
Post a Comment
Subscribe to Post Comments [Atom]
<< Home