Isra’ila na shirin takaita kiran Sallah
Firaministan Isra’ila Benyamin Netanyahu ya goyi bayan wani kudirin doka da ke magana akan takaita kiran Sallah a Masallatan Kudus da na sassan kasar, matakin da kungiyoyin kare hakkin bil’adama suka danganta a matsayin barazana ga ‘yancin gudanar da addini.
Netanyahu ya amince da kudirin dokar ne a lokacin da ya ke ganawa da ministocinsa.
Kudirin yanzu na shirin tsallake karatu na uku a Majalisa kafin ya zama doka, wanda ya kunshi haramta yin amfani da lasifika a lokacin kiran sallah.
Kafofin yada labaran Isra’ila sun ruwaito Netanyahu na cewa ya goyi bayan matakin ne saboda yadda kiran sallan ke damun ‘yan kasa.
Larabawa dai sun kunshi kashi 17.5 na al’ummar Isra’ila yawancinsu Falasdinawa musulmi a gabashin birnin Kudus da ke zargin Yahudawa na danne su.
Source: RFI HAUSA
Labels: news
0 Comments:
Post a Comment
Subscribe to Post Comments [Atom]
<< Home