Monday, November 14, 2016

Za mu ci gaba da kai hare-hare- Shekau


Shugaban Kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau ya ce za su ci gaba da kai hare hare a Najeriya da makwabtanta a cikin wani sakon bidiyo da aka wallafa a kafar You Tube.


Sakon bidiyon na dauke ne da muryar Shekau na tsawon awa daya, kuma a cikin bayaninsa ya dauki alhakin hare-haren ta’addanci na kwanakin baya da aka kai a Borno inda aka samu hasarar rayukan sojoji da fararen hula.

Sannan Shekau ya yi barazanar kaddamar da wasu hare-haren a Najeriya da makwabtanta.

Sai dai kuma Shekau ya shafe lokaci mai tsawo yana wa’azi akan da’awar kungiyarsu ta Boko Haram.

Sannan a ciki ya ambaci sunan sabon shugaban Amurka Donald Trump yana mai cewa yaki yanzu aka fara.

Wannan dai na zuwa ne a dai dai lokacin da rundunar sojin na Najeriya ke ci gaba da kokarin kawo karshen kungiyar ta Boko Haram wadda ta kashe mutane fiye da dubu 20 a cikin shekaru bakwai da suka gabata.

Labels: ,

0 Comments:

Post a Comment

Subscribe to Post Comments [Atom]

<< Home