Wednesday, November 16, 2016

Ce-ce-ku-ce ya barke tsakanin Atiku da El-rufa'i

Gwamnan jihar Kaduna da ke Najeriya, Nasir El-Rufai ya yi zargin cewa tsohon mataimakin shugaban kasar Alhaji Atiku Abubakar yana yin zagon-kasa ga gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari.


El-Rufai na yin raddi ne ga a zargin da Atiku ya yi masa na saba wa ka'idojin aikin gwamnati a lokacin da yake rike da mukamai a gwamnatin Olusegun Obasanjo, sannan ya ce ya yi masa butulci.

A wata hira da Premium Times ta wallafa, Atiku ya ce shi ya shigar da El-Rufai gwamnati har ya zama minista, amma da shi "aka yi amfani wurin zargina da cin hanci", abin da kotu ta wanke ni daga baya.

Sai dai a wata sanarwa da ya fitar, gwamnan El-Rufai ya yi zargin cewa cin hanci da rashawa sun dabaibaye Atiku, abin da ya sa yake tsoron zuwa Amurka.

Ya ce kamata ya yi wa duniya bayani kan rahoton binciken da wani kwamitin majalisar dokokin Amurka ya yi kan yadda aka shigar da fiye da $40m na kamfanin Siemens cikin kasar, kuma aka sanya su a asusunsa da na daya daga cikin matansa.

Amma ana sa bangaren Atiku ya ce babu gaskiya a lamarin: "Wannan rashin adalci ne a rinka zargin mutum ba tare da hujja ba".

Nasir El-Rufai ya ce, "Alhaji Atiku yana son yin takarar shugabancin Najeriya a shekarar 2019 shi ya sa yake tunanin idan ya bata mana suna zai kai gaci.

Jarabar da yake da ita ta son yin mulki ce ta sanya ya goyi bayan 'yan majalisar dokokin da suka yi wa jam'iyyarmu bore, wanda kuma hakan ke ci gaba domin kawai nuna rashin da'a ga shugaban kasa".

Gwamnan na jihar Kaduna ya kara da cewa ya goyi bayan Shugaba Buhari a zaben da ya wuce kuma zai ci gaba da goyon bayansa domin fitar da Najeriya daga kangin da ta fada a ciki.

Tuni dai jam'iyyar APC ta fara daukar dumi saboda wasu batutuwa da wasu ke alakanta wa da kokarin neman iko a zabe mai zuwa na 2019.

Shi ma uban jam'iyyar Sanata Ahmed Bola Tinubu ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda abubuwa ke gudana.

Ba wannan ne karon farko da Atiku da El-Rufa'i ke yin sa'insa ba, sai dai wasu na mamakin dalili da kuma tasirin da hakan ka iya yi a fagen siyasar kasar a wannan karon.

Source: BBC

Labels: ,

0 Comments:

Post a Comment

Subscribe to Post Comments [Atom]

<< Home