Kalli yadda ma taimakin gwamna ya fafata da wasu direbobi
Mataimakin Gwamnan jihar Imo Yarima Eze Madumere yayi wani abin san barka wanda ba kowanne shugaba zai iya aikatawa ba.
Shi dai mataimakin Gwamnan yana kan haryasa ta zuwa aiki ne da yammacin ranar juma’a 11 ga watan Nuwamba lokacin daya hangi wasu jami’an rudunar tsaro ta farin kaya wato Civil Defence suna rikici da wasu direbobin tirela.
Da mataimakin gwamnan yaga haka sai ya tsayar da tawagarsa inda ya sauka yaji kadin dalilin daya hada rikicin, da ake yi ma mataimakin gwamnan bayani, rikicin ya samo asali ne lokacin da wani direba mai suna Nnamdi ya watsa ma wani babban jami’in gwamnatin jihar Imo ruwan leda, sai jami’an tsaron dake gadinsa suka bukaci direban motar ya tsaya, shi kuwa direban daya lura jami’an tsaro ne sai yayi kunnen uwar shegu yaki tsayawa, daga nan ne rikicin ya fara.
A maimakon direbobin su tsaya sai ma suka gitta motocin su akan titi inda suka rufe hanyar Orlu, tsakanin gidan marayun Red Cross da babban kotu, nan da nan cunkoson ababen hawa ya hadu.
Daga nan ne mataimakin Gwamnan ya sulhuntasu, sa’annan ya bukaci direban motar daya dauke Tirelarsa daga kan hanya, nan da nan kuwa cunkoson ya ragu.
A gaskiya wannan shugaban ya cancanci jinjina.
Source: Naij Hausa
0 Comments:
Post a Comment
Subscribe to Post Comments [Atom]
<< Home